Babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ya zartas da wani kudiri na neman kasar Rasha da ta janye sojojinta da kuma kawo karshen ayyukan soji a Ukraine. Hakan na zuwa ne a jajibirin cika shekara ta farko da tsoma bakin sojin Rasha.
Kasashe 141 mambobi ne suka kada kuri'ar amincewa da kudurin yayin da 7 suka nuna adawa da shi. Kasashe 32 ne suka ki kada kuri’a.
advertisement
Indiya dai, bisa yanayin da ta ke da shi a baya kan wannan batu, ta kaurace wa kada kuri'ar adawa da Rasha tare da bayar da shawarar zaman lafiya ta hanyar diflomasiyya da tattaunawa.
***
advertisement